IQNA

Kira Ga Masarautar Saudiyya Da Ta Dakatar Da Shirin Sare Kawunan Fararen 14

23:42 - August 11, 2017
Lambar Labari: 3481788
Bangaren kasa da kasa, jaridar Financial Times ta ce kungiyoyin kare hakkin bila adama da daman a duniya suna kiran Saudiyya da ta dakatar da yunkurin sare kawunan fararen hula 14 da take shirin yi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar Financial Times ta kasar Birtaniya ta bayar da wani rahoto da ke cewa, manyan kungiyoyin kare hakkin bila adama na kasa da kasa suna yin tir da Allah wadai da yanke hukuncin kisa akan fararen hula 14 da masarautar Saudiyya ta yi saboda dalilai na siyasa da bangaranci na akida.

Rahoton ya ce kungiyoyin sun kirayi masarautar Al saud da ta dakatar da yunkurin sare kawunan wadannan fararen hula 14 da take shirin yi babu gaira ba sabat, domin kuwa zartar da wannan hukunci zai kara tabbatar wa duniya da cewa wannan masarauta ta mulkin kama karya ce.

Kotun masarautar gidan sarautar Al saud dai ta yanke hukuncin kisa akan wadannan mutane 14 wadanda dukkaninsu mabiya mazhabar shi'a ne, bisa hujjar cewa sun shiga zanga-zangar nuna rashin gamsuwa da tsarin masarautar kasar, wanda ke haramta musu hakkokinsu a matsayinsu na 'yan kasa.

Mahaifiyar daya daga cikin wadanda masarautar Saudiyya ke shirin sare ma kai mai suna Mujtaba Al-sukuit ta bayyana cewa, Mujataba shi kadai ne ta haifa, kuma mahukuntan kasar sun kame shi yana da shekaru 17 isa hujjar cewa ya shiga zanga-zangar adawa da Al saud a kan haka suka yanke masa hukuncin kisa, a daidai lokacin da wata jami'ar kasar Amurka ta sanar da cewa ta dauke shi, bayan da ya aike musu da takardunsa, inda a halin yanzu maimakon tafiya jami'a, masarautar Al saud na shirin sare masa kai.

3629053

captcha