IQNA

Sayyid Nasrallah:

Kashin Da Isra'ila Za Ta Sha A Yaki Na Gaba Zai Fi Muni

22:05 - August 13, 2017
Lambar Labari: 3481792
Bangaren kasa da kasa, Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana cewar zamanin barazanar 'Isra'ila' ya wuce kuma ba zai dawo ba har abada, don kuwa ta san cewa karfin kungiyar Hizbullah ya karu sama da na lokacin yakin shekara ta 2006.
Kmafanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga tashar alalam cewa, Sayyid Nasrallah ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a yammacin yau don tunawa da shekaru sha daya da nasarar da kungiyar Hizbullah ta samu a kan haramtacciyar kasar Isra'ila a yakin kwanaki 33 da HKI ta kaddamar a kan kasar Labanon a shekara ta 2006 inda ya ce babban dalilin nasarar da dakarun Hizbullah suka samu a kan 'Isra'ilan' shi ne hakuri, tsayin daka, jaruntaka da kuma dogaro da Allah da dakarun suka yi.

Sayyid Nasrallah ya ja kunnen haramtacciyar kasar Isra'ila da cewa matukar dai wani gigi ya sake dibanta ta kawo wa kasar Labanon din hari, to kuwa za su dibi kashinsu a hannu don kuwa dakarun Hizbullah din a shirye suke su mayar mata da martani mai kaushin gaske.

Yayin da ya koma kan kokarin da shugaban Amurka Donald Trump yake yi na matsin lamba ga kungiyar Hizbullah din don biyan bukatar HKI, Sayyid Nasrallah gwamnatin Amurka ba za ta iya raunana irin azama da karfin da dakarun Hizbullah din suke da shi ta hanyar irin wadannan matsin lambar da take wa kungiyar da sauran kawayenta ba.

A watan Yulin shekara ta 2006 ne dai HKI ta kaddamar da yaki kan kasar Labanon bayan da dakarun Hizbullah din suka kame wasu sojojin sahyoniyawan guda biyu, inda a karshen yakin dai da ya dau kwanaki 33 ana yi, dakarun Hizbullah din suka sami gagarumar nasara a kan sojojin sahyoniyawan da hana su cimma kowane guda daga cikin manufofin da suka sanar wanda daya daga cikinsu shi ne kwato wadannan sojoji guda biyu da dakarun Hizbullah din suka kama.

3630040


 


captcha