IQNA

Maniyyata 31 Sun Rasa Rayukansu A Kasar Saudiyya

23:46 - August 14, 2017
Lambar Labari: 3481797
Bangaren kasa da kasa, mahukuntan kasar saudiyya sun sanar da rasuwar maniyyata 31 daga cikin wadanda suka isa kasar domin gudanar da aikin hajjin bana.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin albawwabah cewa, hukumar kula da shige da fice ta kasar Saudiyya ta sanar da cewa, ya zuwa yanzu maniyyata dubu 623 da 313 ne suka isa kasar domin gudanar da aikin hajjin bana daga kasashe daban-daban, amma mutane 31 daga cikinsu sun rasu, duk kuwa da cewa mahukuntan na saudiyya ba su bayyana musabbabin mutuwar maniyyatan ba.

Bayanin ya kara da cewa,a wannan shekara ma’aikatar kula da ayyukan hajji ta kasar Saudiyya ta samar da wasu tsare-tsare dangane da jigilar mahajjata daga kasashen duniya da kuma yadda tsarin tafiyar da lamurran alhazai zai kasance a bana, wanda a cewar hukumar, wannan tsari zai taimaka wajen rage matsaloli da ake fuskanta a yayin aikin hajji.

Dukkanin wadanda za su gudanar da aikin hajjin bana dai bai kai mutane miliyan biyu ba bisa alkalumman da ma’aikatar alhazan kasar Saudiyya ta fitar, alkaluman dai sun ce maniyyata miliyan daya da dubu 384 da 941 ne daga kasashen duniya za su sauke farali, yayin da adadin wadanda za su sauke farali a cikin kasar ta Saudiyya zai kai mutane 567 da 876.

3630302


captcha