IQNA

An Bude Tashar Talabijin Ta Farko Ta Addinin Musulunci A Kenya

23:24 - August 16, 2017
Lambar Labari: 3481803
Bangaren kasa da kasa, an bude tasha talabijin ta farko mallakin musulmi a kasar Kenya wadda za ta rika gabatar da shirye-shirye na addinin muslunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin yada labarai na star cewa, an baiwa wannan tashar talabijin taken fitila ga al’umma, wadda za ta rika yin bayani a cikin shirye-shiryenta a kana bin da ya shafi addinin muslunci da kuma sauran shirye-shirye da suka shafi al’umma baki daya.

Usman warfa shi ne limamin babban masallacin Nairobi, a lokacin da yake gabatar da jawabi a yayin bude wannan tasha ya bayyana cewa, za su yi amfani da wanan dama domin bayyana ma mutane hakikanin addinin muslunci da kuma koyarwarsa, domin kawar da sabanin fahimta da kuma mummunan kallo da ake yi addinin musulunci.

Wannan tasha tana a matsayin tashar addini ta uku a aka bude a kasar, bayan manyan tashshi guda biyu na mabiya addinin kirista, wato tashar GBS da kuma Family TV, wadanda suke gabatar da shirinsu na addinin kirista.

Da dama daga cikin musulmin kasar Kenya sun nuna farin cikinsu matuka dangane da bude wannan tasha, wadda za a ika yin magana da yawunsu, kamar yadda kuma za ta rika bayyana ma al’ummar kasar wadanda mafi yawansu mabiya addinin kirista ne hakikanin muslunci, wanda yake yin kira zuwa ga zaman lafiya da fahimtar juna da kuma girmama dan adam.

3631084


captcha