Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin alalam cewa, a cikin bayanin da kungiyar ta Hizbullah ta fitar, ta bayyana cewa ‘yan ta’addan ISIS suna ta hankoron ganin sun bata wa musulunci suna a idon duniya, tare da bata ma’anar jihadi wanda yake a matsayin aikin ibada mai girma a cikin addinin musulunci.
Kungiya Hizbullah ta mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a harin na Barcelona, tare da yin fatan samun sauki ga wadanda suka samu raunuka sakamkon harin.
A wani bangaren bayanin, kungiyar ta bukaci bangarori na kasa da kasa da su hada karfi da karfe domin tunkarar wannan babbar barazana ta ta’addanin takfiriyya, wanda bai bar kowa ba, musulmi da wand aba musulmi ba, tare da taka wa masu daukar nauyin ta’addanci birki a gabas ta tsakiya da ma a wasu kasashen na duniya.