IQNA

Majalisar Dinkin Duniya Ta Dora Wa Saudiyyah Alhakin Kisan Kisan Yara A Yemen

23:58 - August 18, 2017
Lambar Labari: 3481810
Bangaren kasa da kasa, majalisar dinkin duniya ta dora alhakin kisan daruruwan kananan yara a kasar Yemen a kan gwamnatin Saudiyya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, kamfanin dillancin labaran Associated Press ya bayar da rahoton cewa, Antonio Guterres babban sakataren majalisar dinkin duniya a cikin daftarin rahotonsa dangane da kisan fararen hula a kasar Yemen, ya bayyana cewa, Saudiyya ce ke alhakin kisan mafi yawan kananan yara 1340 da suka mutu sakamakon rikicin Yemen.

Rahoton ya ce mafi yawan kananan yara da suka mutu sakamakon rikicin da ke faruwa a Yemen, sun mutu ne sakamakon hare-haren da jiragen yakin saudiyya suke kaddamarwa a gidajen jama’a, makarantu da kuma asibitoci gami da sauran wuraren hidimomin jama’a na yau da kulluma biranan kasar ta Yemen.

Daftarin rahoton na babban sakataren majalisar dinkin duniya yana kunshe da dalilai da dama da suke tabbatar da hakan, da suka hada rahotannin kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa, da kuma kungiyoyin bayar da agaji masu zaman kansu, wanda komai yake faruwa a gaban idonsu.

An gabatar da wani rahoto wanda kungiyar kare hakkin bil adama ta majalisar dinkin duniya tare da UNICEF suka hada kan kisan kananan yara a duniya, wanda suka bayyana cewa saudiyya ta kashe kananan yara fiye da 600 a tsakanin 2016 da 2017, amma tsohon sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki Moon ya cire sunan kasar saudiyya daga cikin rahoton.

3631706


captcha