IQNA

Addu'oi Ga Watan Suka Rasu Sakamakon harin Barcelona

23:26 - August 19, 2017
Lambar Labari: 3481813
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da addu'oi a masallatai daban-daban da suka hada da na birnin Malaga ga wadanda suka rasu sakamakon harin ta'addanci a Barcelona.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na shafana cewa, a sassan duniya an gudanar da addu'oi ga wadanda harin Barcelona ya rutsa da su.

A nasu bangaren msuulmin kasar ta Spaina bar su a baya wajen yin tin da Allah wadai da wanann hari na ta'addanci, tare ad gudanar da addu'oi ga wadanda suka rasa rayukansu da kuma wadanda suka samu raunuka.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya nuna wasu hotuna da ake gani da suke bayyana yadda msuulmia birnin Malaga na kasar ta Spain suke gudanar da addu'a ga wadanda suka rasu sakamakon harin.

3631887


captcha