IQNA

An Fara Gasar Kur’ani Ta Mata Karo Na Biyar Libya

21:58 - August 20, 2017
Lambar Labari: 3481817
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta mata a kasar Libyada ke gudana a garin Guryan a cikin lardin Jabal Gharbi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na libyaakhbar.com cewa, a jiya an fara gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta mata a garin Guryan a cikin lardin Jabal Gharbi da ke kasar Libya a karo na biyar.

Wannan gasa dai ana gudanar da ita ne a wani hadin gwiwa tsakanin cibiyar taimakon mata ta Mahajjatul Baida da kuma ma’aikatar magajin gari ta birnin.

Khairiyyah Abu Dina ita ce shugabar kungiyar ta kuma bayyana cewa, ya zuwa mutane 304 ne suke a cikin gasar, kuma gasar ta hada dukkanin bangarori.

Mata 278 daga cikin masu gasar ‘yan mata ne, yayin da 26 daga cikinsu kuma dukkaninsu masu aure da iyali, kuma za a kammala gasar ne aranar Alhamis mai zuwa.

3632257


captcha