IQNA

Mafi Yawan 'Yan Ta'adda A Tal Afar Ba Irakawa Ba Ne

22:29 - August 21, 2017
Lambar Labari: 3481820
Bangaren kasa da kasa, Hadi Al-amiri daya daga cikin manyan kwamandojin dakarun sa kai na kasar Iraki ya bayyana cewa, mafi yawan mayakan 'yan ta'addan Daesh da ke cikin garin tal Afar 'yan kasashen ketare ne.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Hadi Amiri ya bayyana cewa, dakarun Iraki da kuma sauran dakarun sa kai na al'ummar Iraki suna ci gaba da yi garin Tal Afar kawanya, wanda yake ahannun 'yan ta'addan na IS, ya ce adadin dukkanin 'yan ta'addan da ke cikin garin bai wuce 1600 zuwa 2000 ba.

Ya ce yanzu haka sun fara kwace iko da wasu unguwanni da suke gefen birnin, wanda hakan zai ba su damar ci gaba da nausawa zuwa cikin birnin, kuma cewarsa yaki da 'yan ta'addan domin tsarkake Tal Afar ba zai dauki wani dogon lokaci ba.

A jiya ne dakarun Iraki suka fara kaddamar da farmakin tsarkake birnin tal Afar daga 'yan ta'addan takfiriyya na Daesh, da ke samun dauki daga wasu gwamnatocin kasashen kasashen larabawa.

3633036


captcha