IQNA

An Gudanar Da Tarukan Tunawa Da Shahadar Imam Jawad (AS) A Kazemain

23:52 - August 22, 2017
Lambar Labari: 3481821
Bangaen kasa da kasa, an gudanar da tarukan tunawa da lokacin zagayowar shahadar Imam Jawad (AS) a birnin Kazemain na kasar Iraki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shain yada labarai na uyun Khalij cewa, an gudanar da wannan taro ne tare da halartar dubban daruruwan masoya manzon Allah (SAW) da iyalan gidansa tsarkaka.

Kamar dai yadda aka saba a taron akn gudanar da jawabai da suka shafi matsyi wadanan bayin Allah, kamar yadda kuma akan gabatar da bege a gare su.

Taron da ya samu alardar dubba daruruwan jaa’a daga ciki da wajen kasar ta Iraki, domin amun abarkacin wannan waliyin Allah jikan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gre shi da iyalan gidana taka.

Imam Jawad (AS) dai da ne ga Imam Redha (AS) kuma dukkaninsu limamai ne daga limaman shiriya na ahlul bait (AS) wadanda suke wakiltar manzon Allah a cikin al’ummarsa. Kamar yadda kuma shi kaka ne ga Imam Mahdi amincin Alah ya tabbata a gare shi kuma ya gaggauta bayyanarsa.

3633172

برگزاری مراسم شهادت جوادالائمه(ع) در کاظمین
برگزاری مراسم شهادت جوادالائمه(ع) در کاظمین
برگزاری مراسم شهادت جوادالائمه(ع) در کاظمین
برگزاری مراسم شهادت جوادالائمه(ع) در کاظمین

captcha