IQNA

Mahardacin Kur’ani Kuma Limami Mafi Karancin Shekaru A Amurka

23:54 - August 22, 2017
Lambar Labari: 3481822
Bangaren kasa da kasa, Hafez Akbar shi ne imami mafi karancin shkaru a kasar Amurka, wada kuma ya hardace ku’ani mai sari tun yana da shekaru 9 da haihuwa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, Hafez Akbar na bayar da limanci ne a masallacin garin Calamzu da ke cikin jaha Michigan a kasar Amurka.

An haife shi ne a kasa Pakistan, kuma ya kammala hardar ur’ani mai tsarki a hannun maiafinsa, wanda hakan ya sa mahaifinsa ya sanya masa sunasa domin jinjina masa.

A shkara ta 2001 ya tafi jami’ar Michigan ta yamma, nda ya karanci injiniya a bangaren wutar lantarki, daga an kuma ya ci gaba da kara fadada bincike a bangarorin ilimin da ya karanta, a cikin shekara ta 2006 ya fara baya da limanci.

Daga biani ya kafa wani shafi na yanar gizo mai suna WSW wanda yake gudana da ayyukan da suka shafi addini da kuma wayar da kan matasa musulmi da ma wadanda ba musulmi ba kan addinin muslunci.

Daga nan kuma ya ci gaba da kara fada ayyukansa a masallacin da yake jagoranta, tare da kokarin nuna wa matasa hakikanin koyarwar manzon Allah (SAW) ta hakika, wanda shi ne addinin muslunci na gaskiya, sabanin abin da ake nuna wa mutane a halin yanzu a kasar a matsayin cewa shi ne addinin musulunci.

Dangane musulmi yana yin amfani da salo daban-daban wajen wayar da kansu, domin kaucewa fadawa cikin yanayi na rudani da kuma bin masu kawo aidun kafita musulmi da raba kan musulmi, wanda hakan ke haifar da kungiyoyin ‘yan ta’adda.

3632470


Mahardacin Kur’ani Kuma Limami Mafi Karancin Shekaru A Amurka
captcha