Stephen O'Brien ya kara da cewa, ya ziyarci yankuna da dama da aka fama da matsaloli na tsaro a kasar, inda ya ce jami'an sojin kasar sun tafka mummunan aikin kisan kiyashi a kan musulmi marassa rinjaye a kasar.
Inda ya ce a mafi yawan wuraren da ya ziyarta, ya samu cewa musulmi sun tsere sun bar dukkanin kaddarorinsu, yayin da sauran jama'a suke wawushe dukiyoyin msuulmi a gaban sojojin gwamnatin kasar, kamar yadda kuma sojojin sukan shiga gaba wajen kisan da ake yi wa musulmin.
Ya bayar da misalign birnin bangasu, inda ya ce an kasha daruruwan musulmi a hannun kungiyoyin masu adawa da musulmi da suke samun dauki daga dakarun kasar, kuma an kore dubban musulmi daga birnin, tare da wawushe dukkanin kaddarorinsu.
Babban jami'in na majalisar dinkin duniya ya ce wajibi ne a gudanar da bincike akn hakikanin abin da ya faru a jamhuriyar Afirka ta tsakiya, tare da gurfanar da dukkanin masu laifi a gaban kuliya.