IQNA

Fararen Hula 30 Sun Yi Shahada A Harin Saudiyya A Kan San'a Yemen

21:59 - August 23, 2017
Lambar Labari: 3481825
Bangaren kasa da kasa, rahotanni daga kasar Yemen sun tabbatar da cewa fararen hula da dama ne suka rasa rayukansu a harin jiragen yakin masarautar saudiyya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Almasirah cewa, fararen hula da dama ne suka rasa rayukansu da suka hada da mata da kananan yara wasu da dama kuma suka jikkata, a hare-haren da jiragen yakin masarautar Al Saud suka kaddamar a yau ranar farko ta wata mai alfarma na Zul Hijjah, a kan birnin san'a na kasar Yemen.

Rahotannin farko dai na cewa jami'an bayar da agajin gaggawa sun isa wurin domin fitar da gawwaki da kuma kokarin ceto wadanda suka jikkata.

Haka nan kuma rahotannin sun ce akwai yiwuwar adadin yaku bisa la'akari da cewa akwai wadanda suke cikin mawuyacin hali.

3633718


captcha