IQNA

Musulmin Amurka Sun Taimaka Ma Wadanda Guguwa Ta Yi Wa Barna

17:30 - September 18, 2017
Lambar Labari: 3481908
Bangaren kasa da kasa, musulmin kasar Amurka sun taimaka ma jama'ar da ambaliyar ruwa ta yi wa barna bayan tsugunnar da su a masallacin Ansari a garin Liverty a jahar Florida.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cbslocal cewa, cibiyar musulmi ta bayar da taimako ga mutane da dama ambaliyar ruwa ta raba su da muhallansu.

An tsugunnar da wasu daga cikin mutane a cikin masallatai, tare da sama musu kayan abinci da bukatar rayuwa na gaggawa domin su samu sukuni a wannan wuri.

Ambalyar ruwan da take tafe da iska tana yin tafiyar saurin kilo mita 240 zuwa 295 a cikin awa daya, wanda aka ya yi sanadiyyar rushewar gidaje da kaddarorin jama'a da na gwamnati da kuma asarori na dukiyar jama'a.

Yanzu haka mahukuntan Amurka na ta kokarn ganin an iya tantance asarorin da wannan babbar guguwar isaka da ruwa ta jawoa cikin wasu yankunan kasar.

3643279


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha