IQNA

Nuna Wa Dalibai Musulmi Wariya A Kasar Denmark

17:58 - September 20, 2017
Lambar Labari: 3481915
Bangaren kasa da kasa, wasu bayanai na nuni da samun matsalolin nuna wariya ga dalibai a wasu makarantu na kasar Denamrk.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na resalehaber cewa, kasar Denmark na daga cikin kasashen turai da suke da tsari mai kyau na koyarwa, amma yanzu an fara samu na nuna wariya ga dalibai musulmi da suke karatu a awasu makarantu na firamare da sakandare mallakin gwamnatin kasar.

Wannan lamari ya bakanta ran wasu daga cikin masana kan harkokin ilimi da suke bin diddigi lamurra a cikin kasashen nahiyar turai, inda suke kallon cewa bullar irin wannan matsala ya sanya ana ganin akwai yiwuwar a samu matsala.

Kasar Denmark ta fara fuskantar bullar wasu kungiyoyin masu tsatsauran ra'ayin kymaar addinin muslunci da kuma baki masu zuwa kasar, wanda hakan yake nuna yadda ake samun karuwar masu gaba da addini a cikin kasashen turaia wannan lokaci.

Guguwar kyamar msulunci ta fara kadawa ne tun kimanin shekaru biyar da suka gabata acikin kasashen turai, amma lamarin ya kara tsananta ne bayan da shugaban amurka mai ci yanzu ya dare kan kujerar mulki.

Babbar barazanar kyamar muslunci dai tana a matsayin wani abu mai matukar tayar da hankali da kuma mayar da hannun agogo baya azamantakewar al'ummomi a nahiyar.

3644417


captcha