IQNA

Musulmin Amurka Sun Yi Aiki Da Hadisin Ma'aiki

16:27 - September 24, 2017
Lambar Labari: 3481928
Bangaren kasa da kasa, musulmin jahar Michigan a kasar Amurka sun yi aiki da umarnin ma'aiki na taimaka ma mutane da suke bukatar taimako.
Kamfanin dillancin labarn iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na nbc25news cewa, Shouna Siddiqi day ace daga cikin wadanda suke jagorantar lamarin musulmi a yankin ta bayyana cewa, sun tara kudade domin taimaka wadanda ambaliyar ruwa ta rutsa da su.

Ta ci gaba da cewa, taimako a cikin addinin muslunci abu ne da ya samo asali daga koyarwar manzon Allah (SAW) inda yake umartar musulmi da su zama masu taimakon mutane a duk lokacin da suka ga mabukaci ko wani da ya shiga cikin matsala yana bukatar taimako.

Ganin irin halin da mutane suka shiga sakamakon ambaliyar ruwa da kuma guguwar isaka a wasu yankuna, wannan yasanya musulmi hada taimako domin bayarwa ga wadanda lamarin ya shafa kamar yadda addinin muslunci ya yi umarni.

A cikin 'yan kwanakin nan dai an yi fama da guguwar isaka da ta yi barna mai tsanani a wasu yankuna na cikin kasar Amurka, inda mutane da dama suka rasa rayukansu, wasu kuma suka yi hasa da kaddarori.

An kiyasta asarar da ak ayi da cewa ta kai da biliyoyin daloli a kasar a yankunan da lamarin ya shafa a musamman ma marassa karfi da basu da gidaje na siminti.

3645294



شیفت شب ساعت 21//عملی‌کردن حدیث نبوی در آمریکا + عکس

شیفت شب ساعت 21//عملی‌کردن حدیث نبوی در آمریکا + عکس

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha