Masu gudana da jerin gwanon, sun rika bayar da abubuwan sha kamar lemun kwalba da abinci ga jama’a da suke wucewa a gefen titi.
Ali Uran daya ne daga cikin wadands suka shirya wannan jerin gwano ya bayyana cewa, lamarin Imam Hussain (AS) lamari ne na al’ummar musulmi baki daya, saboda haka wannan bai kebantu da mabiya mazhabar ahul bait ba kawai.
Ya ci gaa da cewa, yau imanin hekaru ashirin da tara enan suna guanar da taruka na tunawa da juyayin shahadar Imam Hussain a wannan birni, kuma a kullum jama’a suna kara fahimtar abin da ake ciki na daga zaluncin da Imam ya fuskanta daga makiya muslunci.
Haka nan kuma ya yi ishara da darussan da rayuwar Imam Hussain (AS) take koyar da ‘yan adam baki daya ba ma musulmi kawai ba, kan cewa nasara a cikin kowane lamari shi ne juriya da dagewa a kansa, tare da kin mika wuya ga mas adawa da lamarin.