Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran AP cewa, yaron mai sun asheikh Amad yana karatun kur’ani a lokaci guda kuma hawaye na zuba daga idanunsa.
Hotunan dai sun nuna yadda wannan yaro yak cikin damuwa dangane da irin halin da y samu kansa a ciki tare da ‘yan uwansa da kuma iyayensa, bayan kisan kiyashin da aka yi musu a cikin kasarsu ta Myanamr.
Yanzu haka dai akwai dubban daruruwan musulmi ‘yan kabilar Rohingya da aka kora ko kuma suka tsere daga kasar Mayanar domin tsira da rayuaknsu daga kisan da sojojin gwamnatin kasar ke yi musu.
Majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa halin da ‘yan gudun hijirar suke ciki yana da uni matuka, musamman ganin cewa suna a wuri ne wanda babu tantuna kuma gashi lokacin saukar ruwan sama ne.
Kamfanin dilalncin labaran Associated Press ne da ya dauki wadannan hotuna tare da nuna ma duniya halin da wadannan bayin Allah suke ciki.