Sheikh Jalal shi ne shuagaban makarantar Imam Sadiq (AS) kuma shi ne ya gabatar da jawabia wurin tare da halartar mabiya tafarkin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka.
An gabatar da jawaban ne a cikin harsunan farisanci da larabci kasantuwar cibiyar tana gudanar da wani shiri na koyar da harshen farisanci a wurin ga dalibai da dama, wadanda a halin yanzu suna fahimtar harshen.
Shugaban karamin ofishin jakandancin Iran tare da wasu daga cikin malamai sun halrci wurin gudanar da wannan taron makoki.