IQNA

Wasu Masana Daga Senegal Sun Ziyarci IQNA

23:04 - October 08, 2017
1
Lambar Labari: 3481978
Bangaren kasa da kasa, Jim Drami da Sulaiman Gey wasu masana biyu daga kasar Senegal sn ziyarci babban ofishin kamfanin dillancin labaran kur’ani na Iqna.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Sulaiman Gey babban daraktan cibiyar gudanar da bincike a kan harkokin muslunci da ke birnin Dakar fadar mulkin kasar Senegal da kuma Jim Drami wani masani kan harkokin muslunci, sun kai ziyara a babban ofishin kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna a birnin Tehran na kasar Iran, domin ganewa idanunsu ayyukan da ake gudanarwa a wurin.

Wadannan masana biyu dukkaninsu dai sun yi karatu ne a bababr jami’ar muslunci ta kasar Masar wato Azhar, inda a halin yanzu suna daga cikin fitattun masana kan harkokin bincike da kuma rubuta kan ilmomin muslunci a kasar Senegal.

Abin tni a nan dai shi ne wadannan mutane Jim Drami da kuma Sulaiman Gey sun zo Iran ne bisa gayyatar da suka samu daga cibiyar yada aladun muslunci ta Iran, inda suka zo domin haduwa da masana a Iran da kuma ganin irin rubuce-rubucen da aka yin a tafsiri da sauransu a bangarori na addini.

3650430


Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
MUHAMMAD SANI ALIYU GUSAU
0
0
HAKAN YAYI KYAW ALLAH YAQARA BASIRA
captcha