IQNA

Mutane 50 Sun Mutu A Harin Bam A Nigeria

23:52 - November 21, 2017
Lambar Labari: 3482121
Bangaren kasa da kasa, 'Yan sanda a jihar Adamawa dake arewa maso gabashin Najeriya sun ce a kalla mutum hamsin ne suka gamu da ajalinsu a wani harin kunar bakin wake da aka kai a garin Mubi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Harin dai an kai shi ne da asubahin yau Talata a wani masallaci dake garin na Mubu, kamar yadda kakakin 'yan sandan yankin, Osman Abubakar, ya shaidawa kamfanin dillancin labaren Faransa na AFP.

Tun da farko dai alkalumman da hukumar agajin gaggawa a yankin ta fitar sun ce kimanin mutane 15 ne suka rasa rayukansu a harin.

Kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, sai dai sau tarin yawa akan danganta ire-iren wadanan ayyukan ta'adi ga kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram.

3665551


captcha