IQNA

Palastinawa Sun Sake Komawa Kan Teburin Tattaunawa A Kahira

23:55 - November 21, 2017
Lambar Labari: 3482122
Bangaren kasa da kasa, kungiyoyin palastinawa sun hadu a birnin Alkahira na kasar Masar domin ci gaba da tattaunawar sulhu a tsakaninsu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yana gizo na plestine cewa, a yau kungiyoyin palastinawa sun hadu a birnin Alkahira na kasar Masar domin ci gaba da tattaunawar sulhu a tsakaninsu a karkashin kulawar gwamnatin kasar ta Masar.

Bayanin ya ci gaba da cewa, wakilan manyan kungiyoyin palastinawa 13 ne suke halatar wannan zaman taro, inda suke tattauna muhimman lamurra da suka shafi palastinu da al’ummarta, da kuma yadda za su warware matsalolin da ke tsakaninsu ta hanyar tattaunawa da fahimtar juna.

Kungiyar Fatah wadda ita ce babbar kungiyar palastinawa da take rike da gwamnati a yankunan palastinu musamman a gabar yamma da kogin Jordan da kuma quds, ta bayyana fatan ganin wannan ya zama sanadin kawo karshen rikic tsakanin kungiyoyin palastinawa.

3665517


captcha