IQNA

Al’ummar Algeria Sun Tarbi Watan Maulidin Manzon Allah SAW) Da Taruka

23:00 - November 23, 2017
Lambar Labari: 3482131
Bangaren kasa da kasa, hukumar kula da harkokin addini a kasar Algeria ta sana da cewa tun daga lokacin shigowar watan maulidin manzon Allah aka fara gudanar da taruka.

Kamfanin dillancin labara iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran Algeria ya bayar da rahoton cewa, Sayyid Zuhair Buzira babban daraktan hukumar kula da harkokin addini a kasar Algeria ya sana da cewa, hukumarsa tana shirya taruka tun daga lokacin shigowar watan maulidin manzon Allah, da suka hada da gasar kur’ai da hadisi.

Daga cikin ayyukan da ake gudanarwa a cikin wadanan kwanaki masu abarka, har da shirya gasar karatu da kuma hardar kur’ani mai tsarki wadda kan hadamakaranta da mahardata kur’ani, haka nan kuma akwai gasar hardar hadisan ma’aiki.

Kasar Algeria dai tana daga cikin kasashen arewacin nahiyar Afirka da suka nisa wajen raya maulidin manzon Allah (SAW) tun tsawon shekaru, musamman ma yadda darikokin sufaye suka yi tasiria acikin harkokin yau da kullum na al’umma, wanda hakan ya kara sanya son manzon Allah ya yi tasiria cikin zutakan jama’a.

3666157


captcha