IQNA

Marassa Lafiya Kimanin 13400 Suka Rasu Sakamakon Killace Yemen

23:45 - November 24, 2017
Lambar Labari: 3482134
Bangaren kasa da kasa, alkalumman da ma’aikatar lafiya ta kasar Yemen ta bayar sun tabbatar da cewa fiye da mutane dubu 13 ne suka rasu sakamakon killace iyakokin kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na alalam cewa, alkalumman da ma’aikatar lafiya ta kasar Yemen ta bayar a ukumance sun tabbatar da cewa fiye da marasa lafiya dubu 13 ne suka rasu sakamakon killace iyakokin kasar ta sama da kasa da kuma da kawancen makiya al’ummar Yemen karkashin jagorancin Saudiyya ke yi.

Bayanin ya ce tun bayan da Saudiyya ta fara kaddamar da hari kan al’ummar kasar ta Yemen fiye da shekaru biyu da suka gabata, yanzu haka akwai mutane fararen hula wadanda suke da bukata a fitar da su waje domin samun magani, amma hakan bata samu saboda hare-haren Saudiyya da kuma killace dukkanin hanyoyin fita daga kasar.

Baya ga kasha farare hula kusan dubu ashin sakamakon hare-haren ta’addancin Saudiyya kan al’ummar Ymen, wasu dubu 13 da 400 kuma sun mutu ne sakamakon rashin magunguna da Saudiyya ta haramta musu.

3666450


captcha