IQNA

An Girmama Wadanda Suka Halarci Gasar Kur’ani Ta Kasar Oman

23:55 - November 30, 2017
Lambar Labari: 3482154
Bangaren kasa da kasa, cibiyar kula da harkokin al’adu da sarki Qabus a Oman ta sanar da cewa an gimama wadanda suka halrci gasa kur’ani ta kasar.
An Girmama Wadanda Suka Halarci Gasar Kur’ani Ta Kasar OmanKamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar Times f Oman ta bayar da rahoton cewa, angudanar da taron ne a jiya a masalacin sarki Qabus da ke Bushr a cikin kasar ta Oman.

Mahardata 2156 ne suka halarci wanann gasa ta kasa baki daya, wamda hakan ke nuni da cewa adadin ya rubanya na shekarar da ta gabata da ma sauran shekarun baya da aka kwashe ana gudanar da gasar.

Akalai uku n suka jagoranci kwamitin akalan da suka gudanar da akalaci a gasar.

An kuma gudanar da gasa ne a bangarori daban-daban, da suka hada da harda kur’ani baki daya, hardar juzui 24, da juzui 16, da juzui 12, da juzui 6 da kuma juzui biyu.

An grmamam dukkanin wadanda suka halarci gasar, kamar yadda kuma aka bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka fi nuna kwazo.

Shkaru ashirin da bakwai kenan ana gudanar da wannan gasa a kaar Oman a matsayin gasar hardar kur’ani ta kasa bai daya, babbar manufar yin hakan dai ita ce kara zaburar da matasa da kuma karfafa musu gwiwa ka muhimman mayar da hankali ga lamarin kur’ani mai tsarki.

3668352


captcha