IQNA

A Taron Makon Hadin kai:

Babban Malamin Tanzania Ya Jaddada Wajabcin Hadin Kan Al’ummar Musulmi

23:44 - December 06, 2017
Lambar Labari: 3482173
Bangaen kasa da kasa, Sheikh Musa Salim Hadi babban mai bayar da fatawa na kasar Tazania ya bayyana muhimmancin da hadin kai yake da shi a tsakanin al’ummar musulmi.

Babban Malamin Tanzania Ya Jaddada Wajabcin Hadin Kan Al’ummar MusulmiKamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a yayin da yake gabatar da jawabi a gaban taron maon hadin kai a yau a birnin Teran, Sheikh Musa Saim Hadi babban mai bayar da fatawa na kasar Tazania ya bayyana muhimmancin da hadin kai yake da shi a tsakanin al’ummar musulmi, musamman a wannan lokaci da aka tarwatsa al’ummar musulmi.

Malain ya ci gaba da cewa, ko shakka babu, hadin kan al’ummar musulmi a wannan lokaci shi e yafi komai muhimamni, domin kuwa makiya basu damar tarwatsa musulmi ba har sai da suka rarraba kawukansu.

Ya kara da cewa, babban abin bakin cikin shi e yadda wasu daga cikin kasashen musulmi suka zama su ne a kan gaba wajen mara baya ga yahudawa tare da hada kai da su domin wagaza kasashen musulmi da shelanta yaki a  kan kan kasashen da haifar musu da fitana ta ‘yan ta’adda da sauransu, domin kawai su burge yahudawa da Amurka.

Daga karshe ya yi jinjina ga marigayi Imam Khomeini wanda ya assasa makon hadin a cikin watan rabiul awwal watan maulidin manzon Allah, kasatuwar manzn Alah shi ne ya hada dukkanin musulmi, a kan haka Imam Khomeini ya zabi wannan wata mai albarka kuma ranakun makon haihiwar mazon Allah ya kira shi da makon hadin kan musulmi.

3670099

 

 

 

captcha