IQNA

Jami’an Tsaron Masar Sun Dauki Matakan Tsaro A Kusa Da Masallacin Imam Hussain (AS)

23:05 - January 12, 2018
Lambar Labari: 3482290
Bangaren kasa da kasa, jami’an tsaron kasar Masar sun dauki kwararan matakan tsaro a kusa da masallacin Imam Hussain (AS) da ke birnin Alkhira a daidai lokacin da ake tarukan tunawa da kawo kan Imam Hussain (AS).

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tun daga jiya jami’an tsaron kasar Masar suka fara daukar kwararan matakan tsaro a kusa da masallacin Imam Hussain (AS) da ke birnin Alkhira a lokacin da aka fara tarukan tunawa da kawo kan Imam Hussain (AS) zuwa birnin kamar yadda wasu daga cikin al’ummomin Masar suke cewa.

Wannan taro ana gudanar da shi a kowace sekara tsawon daruruwan shekaru, inda mabiya darikun sufaye da mabiya mazhabar shi’ar Ahlul bat (AS) suke taruwa suna gudanar da taruka na tunawa da abin da ya faru da Imam Hussain (AS) da iyalan gidan manzon Allah (SAW) a kowace shekara a daidai lokaci irin wannan.

‘Yan darika da kuma ‘yan shi’ar ahlul bait a Masar sun yi imanin cewa, bayan kasha Imam Hussain (AS) an kai kansa mai albarka zuwa fadar Yazid a Damascus a Syria, amma daga bisani sarakunan Fatimiyya sun dauko kan sun dawo da shi Masar, kuma a inda yake aka gina masallacin Imam Hussain (AS) a cikin Alkahira.

Sibt Ibn Jauzi wanda ya rasu a shekarar (654) hijira kamariyya, daya daga cikin manyan malaman sunnah ya bayyana cewa, sarakun Fatimiyya sun dauko Imam Hussain dan Imam Ali daga babul Faradis dake Damascus zuwa Askalan a c ikin Palastine, daga nan kuma suka dauko shi zuwa Alkahira.

3681247

 

 

captcha