IQNA

An Fara Taron Nuna Goyon Baya Ga Quds A Kasar Tunusia

22:47 - January 20, 2018
Lambar Labari: 3482317
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wani taro na nuna goyon baya ga Quds a kasar Tunisia tare da halartar kungiyoyin farar hula.

Kamfanin dillancin labaran Safa ya bayar da rahoton cewa, dubban jama'a ne suka taru yau domin gudanar da wani taro na nuna goyon baya ga Quds a kasar Tunisia.

Babbar manufar taron dai ita ce nuna goyon baya ga masallacin Quds mai alfarma da kuma dukkanin al'ummar palastinu da ke karkashin mulkin mamaya na haramtacciyar gwamnatin yauhudawa.

Baya ga kuma su nuna rashin amincewarsu da matakin da shugaban kasar Amurka ya dauka na shelanta birnin Quds mai alfarma a matsayin fadar mulkin haratacciyar kasar Isra'ila, lamarin da ya bakantawa dukkanin musulmi.

Kasar Tunisia na daga cikin kasashen da suka nuna rashin amincewarsu da wannan mataki a hukumance, tare da bayyana matakin na shugaban Amurka da cewa ya wuce gona da iri.

Yanzu haka dai kungiyoyin farar hula da na kwadogo gami da na kare hakkin bil adama fiye da hamsin ne suka taru domin gudanar da wannan taro a kasar ta Tunsia.

Kamar yadda kuma jama'ar gari da dama ne suma suka shiga cikin lamarin, domin tattabar da goyon bayansu ga al'ummar palastinu da kuma masallacin Quds mai alfarma.

3683680

 

 

 

captcha