Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na Times Headline cewa, an fara gudanar da kamfe mai take #StrongInHijab domin zagayowar ranar hijabi ta duniya.
Mata musulmia koina cikin fadin duniya rubuta abin da suke bukata fada dangane da hijabi suna turawa shafukan zumunta.
A ranar hijabi ta duniya mata suna saka nauoin hijabi tare da gudanar da taruka na wayar da kai kan muhimmanci hijabi da kuma matsayinsa a cikin addinin muslunci.
Haka nan kuma mata sukan bayar da kyautuka na musamman ga ‘yan uwansu mata wadada ba musulmi ba, tare da gayyatarsu zuwa gidajensu ko kuma wasu wuraren taruka na musamman da ake shiryawa a ranar kan hijabi.
A kan bayar da hijabi ga masu bukata domin saka a wannan ranar, domin su ji yadda musulmi suke ji, domin su gane cewa hijabi tufafi ne ba wani abin tsoro bane, domin su daina yi musulmi mata masu yin lullubi wani kallo na daban.
Dukkanin addinai da aka saukar daga sama dai sun yi umarni da saka hijabi, kamar yadda addinin musulunci da ya zo karfafa wannan lamari kamar yadda yake a sauran addinai da aka saukar daga sama.
An fara gudanar da ranar hijai ne cikin shekara ta 2013 a kasar Amurka, sakamkon cin zarain da mata musulmi masu saka lullubi suke fuskata daga wasu masu kyamar musulunci.