IQNA

Za A Gina Gidaje 14,000 Ga Yahudawan Sahyuniya

22:55 - January 22, 2018
Lambar Labari: 3482325
Bangaren kasa da kasa, haramtacciyar kasar Isra'ila na shirin gina wasu gidaje guda 14,000 a cikin yankunan palastinawa da ke cikin birnin Quds mai alfarma.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na safa cewa, karamar majalisar dokokin Isra'ila ta amince da gina wasu sabbin matsugunnan yahudawa 'yan share wuri zauna a cikin yankunan Palastinawa a birnin Quds.

Majalisar ta ta yahudawan sahyuniya ta bijiro da batunne kwana daya bayan amincewar Trump da birnin Quds a matsayin fadar mulkin yahudawan sahyuniya.

Da dama daga cikin 'yan majalisar dai suna ganin cewa wata babbr dama ce da bai kamata su yi wasa da it aba, domin kuwa  ahalin yanzu suna da cikakken goyon bayan Amurka na yin abin da suka ga dama a cikin yankunan palastinawa ko da duniya ba ta so hakan ba.

Haramtacciyar kasar Isra'ila za ta gina gidajen yahudawa 'yan share wuri zauna guda dubu 7 a cikin yankunan palastinawa da ke gabashin birnin Quds, sauran kuma za ta gina a su a cikin wasu matsugunnan da dama ta riga ta gina su bayan ammaye yankunan na palastinwa a Quds.

Tun bayan da Trump ya shelanta birnin Quds mai alfarma  a matsayin fadar mulkin haramtacciyar kasar Isra'ila, duniya ke ci gaba da yin Allah wadai da hakan.

3670514

 

 

 

captcha