Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na CAIR cewa, Couchnisky wani jami’i ne a garin Jackman cikin jahar Mine, wanda ya bayyana musulmi a matsayin mutane marassa kan gado masu kama da dabboi.
Wannan furuci ya fuskanci kakkausar suka da martani mai zafi daga cibiyar musulmin kasar ta Amurka, tare da bayyana hakan a matsayin babban abin takaici.
Cibiyar ta kara da cewa, kyamar musulmi ko baki ‘yan kasashen ketare a kasar Amurka an san hakan ne daga wasu ‘yan tsirarun mutane a lokutan baya, amma a yanzu a kasar Amurka tun bayan zaben da aka yi hakan ya zama matsayar gwamnati, kuma jami’an gwamnatin Amurka ne suka kara ruruta wutar kyamar musulmi a kasar a halin yanzu.
Bayanin cibiyar ya ce wannan furuciabin takaici ne, kuma ya dace a yi Allah wadaida hakan matukar dai ana fatan ganin Amurka ta ci gaba da wanzuwa a matsayin kasa ta dimukradiyya.
A cikin makon da ya gabata ma an kori wasu malaman makaranta guda biyu a jahar Texas, saboda tsanin kyamar da suke nuna wa dalibai musulmi da suke karatu a karkashinsu.