IQNA

Littafin Juyin Juya Hali Da Aka Tarjama A Cikin Harshen Faransanc A Senegal

22:33 - January 28, 2018
Lambar Labari: 3482344
Bangaren kasa da kasa, za a gabatar da wani littafi da aka tajama a cikin harshen Farasanci a kasar Senegal.

Littafin Juyin Juya Hali Da Aka Tarjama A Cikin Harshen Faransanc A SenegalKamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shain sadarwa na yanar gizo na bangaren hulda da jama’a a cibiyar yada al’adun muslunci cewa, ana shirin kaddamar da wani littafi da aka tajama a cikin harshen Farasanci a kasar Senegal tare da grmama mutmin da ya yi tarjamar.

Wannan ya zo ne a daidai lokacin da akjue shirin fara gudanar da taruka na kwanaki goma na juyin juya halin muslunci a kasa Iran, wanda yake faraway daga ranar goma sha biyu ga watan Bahman, kuma zai ci gaba har zuwa ashirin da biyu ga watan.

Wadannan dai su ne ranakun juyin juya hali goma wadanda ake kira kwanaki goma na alfijr da Imam Khomeni (RA) ya tabbatar da juyin Islama.

Haka nan kuma za a bayar da dama ga masu rubutun kasidu da kuma marubuta wakoki kan juyi da su gabatar da nasu kokarin, inda za a baya da kyautuka na musamman ga marubuta da kuma wanda ya tarjama littafin juyi.

3685993

 

 

 

 

captcha