IQNA

Makarantar Nasiriyya Ta Rarraba:

Bayanai Kan Juyin Musulunci Ga ‘Yan Kasashen Wajen Ranar 22 Bahman

23:45 - February 11, 2018
Lambar Labari: 3482386
Bangaren kasa da kasa, makarantar Nasiriyyah a birnin Isfahan na kasar Iran ta rarraba wasu bayanai kan juyin juya halin musluni na Iran a ranar 22 Bahman a dandalin Imam Khomeni (RA).

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a daidai lokacin tarukan tunawa da zagayowar ranar juyi a yau, makarantar Nasiriyyah a birnin Isfahan na kasar Iran ta rarraba wasu bayanai kan juyin juya halin musluni na Iran a ranar 22 Bahman a dandalin Imam Khomeni (RA) da k tsakiya birnin ga ‘yan kasashen ketare.

Bayanin ya ci gaba da cewa, makarantar ta bayar da wadannan bayanai ne ga masu zuwa yawon shakatawa, wanda aka tarjama a cikin harsunan turanci da laraci da kuma faransanci.

Daga bayanan akwai kalaman jagoran juyin juya halin musulunci da kuma na marigayi Imam Khomeni (RA) da aka rarraba gare su.

Makarantar Nasiriyya tana da dadaden tarihi wajen karbar baki ‘yan kasashen ketare tare da yi musu bayani kan addinin muslunci, da kuma yi musu bayani kan juyin Islama da aka yi a kasar.

3690571

 

 

captcha