IQNA

Wasu Mutane Sun Kai Farmaki Kan Wani Masallacin Tarihi A Palastinu

23:26 - February 12, 2018
Lambar Labari: 3482389
Bangaren kasa da kasa, wasu mutae da ba a san ko su wane ne ba sun kai farmaki kan masallacin tarihi a cikin lardin Jalil tare da gina wata rijiya a cikinsa.

Wasu Mutane Sun Kai Farmaki Kan Wani Masallacin Tarihi A PalastinuKamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na safa daga Palastinu ya bayar da rahoton cewa, wasu mutae da ba a san ko su wane ne ba sun kai farmaki kan masallacin tarihi a garin Gabisiyya da ke cikin lardin Jalil tare da gina wasu ramu a cikin masallacin.

Wadanda suka ganewa idanunsu sun bayyana cewa, mutanen sun shiga wurin ne da dare dauke kulake da karafa, ba a san ko suwane suka aikata hakan ba.

A ranar Lahadin da ta gabata ma a gari safad inda hubbaen annabi Yusha (AS) magajin annabi Musa (AS) yake, an ci zarafin wasu Palstinawa mazauna gain gasibiyya, lamarin da ya fusata su matuka.

Haramtacciyar gwamnatin yahudawan sahyuniya tana daukar matakan takurawa ga palastinawa da suke zaunea  cikin yankunan da ta mamaye, tare da kafa musu dokoki da kaidoji na muzgunawa.

3690837

 

حمله افراد ناشناس به مسجدی در «الجلیل»

 

حمله افراد ناشناس به مسجدی در «الجلیل»

 

 

 

 

 

 

captcha