Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai vetogate.com ya bayar da rahoton cewa, Ashraf Fahmi daya daga cikin manyan daraktocin ma’aikatarkula da harkokin addni a Masar ya sheda cewa, kasashe 70 ne za su halarci gasar kur’ani ta duniya karo na ashirin da biyar da za a gudanar a kasar.
Ya ce ya zwa alkalai 10 aka tababtar da cewa za su yi alkalanci a gasar, dukkaninsu daga kasashen labawa.
Gasar dai za ta samu halartar wakilai daga kasashen larabawa da na musulmi da kuma kasashen Asia da na turai.
A ranar 24 ga watan Maris 2018 ne za a fara gudanar da gasar ta Masar, wadda za ta dauki tsawon kwanaki shida ana gudanar da ita.