Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, rahotanni sun tabbatar da cewa, manyan bankunan kasar Rasha na Sberbank da kuma babban bankin kasar ne za su shiga gaba wajen fara gwada wannan tsari.
Yanzu haka an cimma yarjejeniya tare da bankin musulunci da kuma wadannan manyan banuka na kasar Rasha kan yadda za a fara aiwatar da shirin, da kuma bangarorin da za a fara gudanar da shi.
A ranar 27 ga wannan wata na Fabarairu ne dai dukkanin bangarorin za su gudanar da zama na musamman domin tattauna wannan batu, da kuma sanin daga inda za a fara.