IQNA

Iran Ta Bayar Da Kyautar Littafai Bugun Hannu Da Suka Hada Da Kur’ani Ga Jami’ar Kufah

23:33 - March 15, 2018
Lambar Labari: 3482475
Bangaren kasa da kasa, Iran ta bayar da kyautar wasu littafai masu kima da ka rubuta da hannu a kasar tun tsawon shekaru masu yawa da suka gabata ga jami’ar ta kasar Iraki.

 

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, karamin ofishin jakadancin Iran a kasar Iraki ne ya mika littafan ga mahukuntan jami’ar ta Kufah, wadda take karkashin kulawar hubbaren Imam Hussain (AS).

Wadannan littafai dai sun hada da wasu kwafin kur’anai da aka rubuta da hannu da hannu, da kuma wasu littafai da suka hada da na fikihu, adabi, usul, hadis, tarihi da sauransu, wadanda za a saka su a bangaren adana littafan tarihi da ke cikin babban dakin karatu na jami’ar.

Bayanin ya ce adadin dukkanin littafan da aka mika ma jami’ar ta Kufah daga jamhuriyar musulunci ta Iran sun ka mujalladi 228, kuma dukkaninsu rubutun hannu n da aka yi daruruwan shearu da suka gabata.

3699628

 

captcha