IQNA

Taro Kan Mahangar Musulunci Dangane Da Sauran Imlmomi A Jami’ar Texas

23:39 - March 15, 2018
Lambar Labari: 3482477
Bangaren kasa da kasa, za a gudana da wani zaman taron karawa juna sani a jami’at San Antonio kan mahangar addinin muslunci dangane da sauran ilmomi da dan adam ke bincike a kansu.

 

Kamfanin illancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gzo na stmarytx.edu cewa, a cikin mako mai zuwa ne za a gudana da wani zaman taron karawa juna sani a jami’at San Antonio da ke jahar Tex ta Amurka, kan mahangar addinin muslunci dangane da sauran ilmomi da dan adam ke bincike a kansu ta fskoki daban-daban.

Salman hami shi ne babban darakta na cibiyar gunadanar da bincike ta musulmin kasar Amurka, shi ne babban mai jawabi a wurin taron, kamar yadda wasu daga cikin masana da za su halarci daga sassa daban-daban na Amurka da latin Amurka za su gabatar da nasu kasidun.

Babbar manufar taron dai ita ce kara fito da matsayin muslunci dangane da ci gaban ilimi a dukaknin bangarori na rayuwar dan adam.

3699899

 

 

 

 

 

 

captcha