IQNA

An Kawo Karshen Shrin Tafsirin Kur’ani A radiyon Kur’ani Na Gaza

21:33 - March 16, 2018
Lambar Labari: 3482480
Bangaren kasa da kasa, an kammala wani shirin kur’ani mai tsarki na tafsiri da aka gabatar a radiyon kur’ani na Gaza a cikin shiri 600.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na safa cewa, a jiya an kammala wani shirin kur’ani mai tsarki na tafsiri da aka gabatar a radiyon kur’ani na Gaza wanda malam Abdulkarim Dahshan ya gabatar.

An fara gudanar da wannan shirin ne tun a cikin shekara ta 2009, inda ake fassara ayoyin kur’ani daki-daki daga sama har zuwa kasa, inda aka kammala wanann shiri na tafsiri a cikin shekaru takwas.

Wannan shiri dai ya samu karbuwa  a wajen jama’a, sakamakon yadda malamin yake gabatar da bayani kan ayoyin kur’ani da darussa da utane za su amfana.

Abdulkarim Dahshan yana daga malaman jami’ar musulunci ta Gaza, ya karatun digiri na biyu a  jami’ar Jordan, daga nan kuma ya nufi jami’ar Khartum a  kasar Sudan, inda ya yi digiri na uku a shekarar 1995, ya kuma yi rubutunsa na karshe a kan kare hakkin bil adama a cikin kur’ani da ruwaya.

3700350

 

 

 

captcha