IQNA

An Samu Wani Dadadden Kur’ani A Kasar Tunisia

23:46 - March 18, 2018
Lambar Labari: 3482484
Bangaren kasa da kasa, baban dakin adana kayan tarihi a kasar Tunisia ya sanar da samun wani kwafin kur’ani da tarihinsa ke komawa zuwa ga karni na bakwai bayan hijira.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na Arabil Jadid cewa, babban dakin adana kayan tarihi na kasar Tunisia bangaren dakin karatu na cibiyar ya sanar da samun wani kwafin kur’ani da tarihinsa ke komawa zuwa ga karni na bakwai bayan hijira wanda ae sa ran na Ibn Gaddus Andulusi ne.

Wannan kur’ani dai an rubuta shi da tawada mai launin kasa, kamar yadda kuma an yi amfani da fasahar rubutu ta musamman wajen rubuta, musamman wajen ajiye ayoyi da kuma alamun karshen aya.

Masana tarihi na kasar Tunisia sun yi imanin cewa wannan kwafin kur’ani ya kai kimanin shekaru dari tara da rubutwa, kuma si ne kur’ani na uku na tarihi da ake da su a halin yanzu a kasar ta Tunisia.

Tun a cikin watan Fabrairun shekarar da ta gabata ce dai bayan samun wannan kwafin kur’an, aka mika shi ga wani wamitin bincike na musamman domin gudanar da bincike a kansa.

3700948

 

 

 

 

 

 

captcha