IQNA

An Harbe Limamin Wani Masallaci A Palastine

23:47 - April 03, 2018
Lambar Labari: 3482538
Bangaren kasa da kasa, Sheikh Muhammad Sa’ada limamin masallacin Tauhid da ke garin Ummul Fahm ya gamu da ajalinsa a yau, bayan da wasu ‘yan bindga suka bude masa wuta.

 

Kamfanin dillancin labaran ma’a ya bayar da rahoton cewa, da jiffin safiyar yau ne wasu ‘yan bindga da ba a san ko su wane ne suka bude wutar bindiga a Sheikh Muhammad sa’ada a lokacin da yake fitowa daga masallacin Tauhid da yake limanci.

Jim kadan bayan faruwar lamarin an yi kokarin kai malamin asibiti, amma rai ya yi halinsa, jami’an tsaro sun iso wurin, kuma sun fara gudanar da bincike, amma babu wani mutum ko wata kungiya da ta dauki alhakin aikata wannan aika-aika.

Haka nan kuma daga bangaren jami’an tsaron babu wani bayani na kame wasu da ake zargin suna da hannua  cikin lamarin.

3702729

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha