Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Quds Al-arabi cewa, Bashir Bin Hassan ya bayyana Muhammad Bin Salman a mtsayin mutumin da ke musu da Allah da manzonsa.
Ya ce a cikin kur'ani mai tsarki Allah ya bayani dalla-dalla dangane da su wane ne bani Isra'ila da kuma yadda suka cutar da annabawan Allah da kisan manzannin Allah, da kuma yadda suka cutar da manzo a Madina, da yadda Allah ya tsine musu saboda zaluncinsa da saba alkawalinsu, amma a yau Bin Salman duk ya yi watsi da wannan fada ta Allah.
Malamin ya ci gaba da cewa, kalaman Bin Salman suna a matsayin halasta ayyuakn ta'addancin da yahudawan Isra'ila suke yi ne kan al'ummar musulmi na palastinu da kuma keta alfarmar wurare masu tsarki na al'ummar musulmi, da suka hada da masallacin aqsa alkiblar msuulmi ta farko.
Daga karshe ya ce kalaman na Bin Salman sun sanya shakku kan hakiaknin manufar zuwan Muhammad Bin Salman a kan kujerar sarautar saudiyya, inda malamin ke ganin cewa akwai wata dasisa da ake shiryawa al'ummar musulmi ta hanyar kawo Bin Salman a kan mulki.
3703378