Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, A bayanin hadin gwiwa da kungiyoyin kare hakkin bil-Adama 13 suka fitar sun bukaci mahukuntan Bahrain da su hanzarta sakin fursunonin siyasa da ake tsare da su a gidajen kurkukun kasar musamman Abdul-Hadi Khawajah.
Tun a ranar tara ga watan Aprilun shekara ta 2011 ne jami'an tsaron kasar Bahrain suka kame Abdul-Hadi Khawajah fitaccen mai kare hakkokin bil-Adama da ke da izinin dan kasa a Denmark kan nuna rashin amincewarsa da jibge sojojin Saudiyya a cikin kasar Bahrain da nufin murkushe zanga-zangar lumana, inda kotu a Bahrain ta zartar da hukuncin daurin rai da rai a kansa.