IQNA

Jagora: Karuwar Matsin Lamba kan Iran Sakamako Ne Na Karuwar Karfinta

23:51 - April 08, 2018
Lambar Labari: 3482552
Bangaren siyasa, jagoran juyin juya halin musulinci na kasar Iran ya bayyana cewa dalilin da ya sanya makiya ke kara matsin lamba kan kasar, saboda tsoratar da suka yi na karfin da kasar tayi.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yanar gizo na jagora habarta cewa, Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya gana da manyan hafsoshin sojin kasar kasar, inda a farko ya meka godiyar ga Allah da ya gwada masa wannan Wata na Rajab mai albarka, inda ya ce watannin Rajab, Sha'aban da Ramadan saboda albarka dake cikinsu, dukkanin ranaikunsu na a matsayin salla ga salihan bayi, kuma kamata ya yi ko wani Bawa na Allah ya amfana  da wadannan watanni masu cike da ma'anawiya.

Jagora, ya bayyana juriya game da tunakarar makiya, tabbatar da tsaro, daukaka alamin musulinci, game da isashen karfi shi ne tushen manufar Dakarun tsaron jamhoriyar musulinci na Iran,kuma dukkanin ayukan da dakarun tsaron kasar ke aiwatarwa wajibi ne ya kasance bisa wannan manufa.

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya ce lokacin da ake ciki a yanzu, lokaci ne na daukakar jamhuriyar musulinci ta Iran, domin haka ne makiyan musulinci suka kara kaimi wajen yin matsin lamba ga kasar, kuma yadda tsarin musulincin kasar ke kara karfi ya firgita makiya.

Har ila yau, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya kara da cewa duk da makirci da kuma makarkashiyar da makiya ke yiwa kasar, karfin tsarin musulinci a ko wata rana kara ci gaba yake.

3704045

 

 

 

captcha