Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza da ke karkashin ikon Hamas ta sanar cewa, a jiya Alhamis sojojin yahudawa Isra’ila sun bude wutar bindiga a yankin Khan Yunus, inda suka kashe Abdullah Al-shahari da shekaru 28 da haihuwa.
Da jijjifin safiyar ranar ta Alhamis ma sojojin Isra’ila sun kaddamar da wani farmakin da jirgein yaki a yankin Shujaiyya, inda a nan ma suka kashe wani bafalstine tare da jikkata wani.
Fiye da Falastinawa 30 ne dai sojojin yahudawan Isra’ila suka kashe tun daga ranar 30 ga watan Maris da ya gabata, ranar Falastinawa suka fara gudanar da gangamin tunawa da cika shekaru arba’in da biyu da kwace musu wasu yankuna da gonaki da filaye da Isra’ila ta yi.