IQNA

An Karrama Yara Mahardata Kur'ani A Masar

23:49 - April 14, 2018
Lambar Labari: 3482570
Bangaren kasa da kasa, an karrama yara 20 mahardata kur'ani a lardin Qana na Masar.

 

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga jaridar aldastur cewa,a  jiya a Masar an karrama yara 20 mahardata kur'ani a  lardin Qana.

Wata cibiyar da take gudanar da ayyukan alhairi ce ta dauki nauyin shirya wannan taro tare da gayyatar wasu mabiya addinin kirista.

Wannan taron dai an karrama dalabai da suka hardace kur'ani mai tsarki da kuma kananan yara guda 20 wadanda suka hardace kur'ani gami da marayu.

An gudanar da wannan shiri ne dai a ranar da ake kira ranar marayu.

3705469

 

 

captcha