IQNA

Wani Mai Fasahar Rubutu Ya Rubuta Kur’ani A Cikin Kwanaki 140 A Masar

23:43 - April 17, 2018
Lambar Labari: 3482577
Bangaren kasa da kasa, Hamdi Bahrawi wani malamin makaranta ne dan shekaru 51 da haihuwa daga yankin Dehqaliya na Masar da ya rubuta kur’ani a cikin kwanaki 140.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na sadal balad ya bayar da rahoton cewa, Hamdi Bahrawi daga yankin Dehqaliya na Masar wanda kuma mai fasahar rubutun larabci ne, ya samu nasarar rubuta cikakken kur’ani a cikin kwanaki 140 da rubutu mai kyau.

Duk da cewa wannan aiki yana da matukar wahala a wajen Bahrawi kasantuwar yana aikin koyarwa, amma duk da haka ya ware wani bangaren lokacinsa domin ganin ya kammala wannan aiki mai matukar kima.

Ya ce a lokacin da ya fara aiki yay i tunain cewa da wahala ya iya kammala shi cikin kankanin lokaci, amma da taimakon Allah y agama a ikin a cikin kwanaki 140 daidai.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, iyalansa sun taka rawa wajen cimma wannan nasara, domin kuwa a owane lokaci su ne suke kara ba shi karfin gwiwa domin ya ci gaba da aikin.

Cibiyar azahar ta amince da wannan kur’ani bayan kwamitin malamai ya duba shi daga farko har karshe.

3706291

موفقیت خوشنویسی مصری در کتابت 140 روزه قرآن

موفقیت خوشنویسی مصری در کتابت 140 روزه قرآن

موفقیت خوشنویسی مصری در کتابت 140 روزه قرآن

موفقیت خوشنویسی مصری در کتابت 140 روزه قرآن

موفقیت خوشنویسی مصری در کتابت 140 روزه قرآن

موفقیت خوشنویسی مصری در کتابت 140 روزه قرآنموفقیت خوشنویسی مصری در کتابت 140 روزه قرآن

موفقیت خوشنویسی مصری در کتابت 140 روزه قرآنموفقیت خوشنویسی مصری در کتابت 140 روزه قرآن

captcha