IQNA

Ibrahim Bah: Akwai Karancin Darussan Kur’ani A Jami’oin Guinea

23:29 - April 23, 2018
Lambar Labari: 3482596
Bangaren kasa da kasa, Ibrahim Bah mahardacin kur’ani ne dan kasar Guinea wanda ya bayyana cewa akwai karancin darussan kur’ani a jami’ion kasar.

 

Ibrahim Bah wanda ya wakilci kasar Guinea a bangaren hardar dukkanin kur’ani a gasar kur’ani ta duniya da ke gudana a Tehran a zantawarsa da kamfanin dillancin labaran iqna ya bayyana cewa, ba a bayar da muhimmanci wajen koyar da darussan kur’ani a jami’oin kasar.

Ya ce mafi yawan wadanda suka samu ilimin kur’ani mai tsarki sun same shi ne ta hanyar makarantun gida da kuma makarantun allo na gargajiya.

Kamar yadda haka lamarin yake a sauran ilmomi na addini wadanda ake koyarwa  makarantu wadanda ba  asamu a jami’a.

Ya ce yanzu yana da shekaru 21 da haihuwa kuma ya hardace kur’ani ne tun yana da shkaru 15 da haihuwa.

Haka nan ya kara cewa, yay i amfani da hanyoyin yanar gizo wajen kara samun bayanai kan kur’ani da kuma kara yautata hardarsa, wanda da matasa za su yi amfani da hanyoyin yanar gizo ta hanyar koyon karatun kur’ani da sun amfana matuka, amma abin ban takaici suna amfani da wannan hanya inda bai kamata ba.

Kasar Guinea da kae yammacin Afrika tana mutane miliyan 10 kimanin kashi chasain cikin dari musulmi ne, 10 kuma cikin dari kiristoci.

3707706

 

 

captcha