IQNA

Tawagogi Daga Ghana Da Zimbabwe Na Halartar Gasar Kur’ani A Tehran

23:31 - April 23, 2018
Lambar Labari: 3482597
Bangaren kasa da kasa, Tawagogi biyu daga kasashen Ghana da Zimbawe na halartar gasar kur’ani ta duniya karo na 35 a birnin Tehran.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga cibiyar yada al’adun muslunci cewa, tare da hadin gwiwa da karamin ofishin jakadancin kasar Iran a Ghana, makaranta da mahardata kur’ani bakawai ne daga kasar suke halartar gasar a dukkanin bangarori na harda da karatu, kuma sun hada da maza da mata da makaho guda.

Kafin su bar kasar Ghana dai sun gana da shugaban karamin ofishin jakadancin Iran da ke kasar ta Ghana Muhammad Hassan Ipekchi.

Wanda ya yi musu bayani da cewa, hakika halartar tawagar kasar Ghana a gasar kur’ani ta duniya da adadin mutane bakawai har da mai larurar gani, hakan wata babbar alama ce kan irin gagarumin ci gaban da aka samu a bangaren himmatuwa da lamarin kur’ani a kasar Ghana.

Daga kasar Zimbabwe ma karamin ofishin jakadancin Iran ya sanar da cewa, Sheikh Arbasa Makalana fitaccen makarancin kur’ani na kasa da kasa dan kasar Zimbabwe ne ke halartar gasar ta duniya a Iran.

Wannan dai shi ne karo na 35 da ake gudanar da wannan gasar kur’ani ta duniya a birnin Tehran, wadda aka bude tun ranar Alhamis da ta gabata, kuma ana gudanar da ita ne a masallacin Imam Khomeini da ke birnin na Tehran.

3707994

 

 

 

captcha