IQNA

Falastinawa Da Dama Ne Suka Samu Raunuka A Dauki Ba Dadin da Sauke Yi Da Sojin Isra’ila

23:33 - April 23, 2018
Lambar Labari: 3482598
Bangaren kasa da kasa, rahotanni daga Palastine sun cewa, Falastinawa da dama suka jikkata sakamakon auka musu da sojojin yahudawan Isra’ila suka yi a yankin Abu Dis da ke gabashin Quds.

 

Kmafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Shafin yada labaran na Al-nashrah ya bayar da rahoton cewa, sojojin yahudawa gami da jami’an ‘yan sandan yahudawan Isra’ila, sun kutsa kai da safiyar yau a yankin Abu Dis, inda suka yi ta bincike a gidajen Falastinawa mazauna yankin, wanda hakan ya harzuka matasa suka shiga arangama da su.

Jami’an tsaron yahudawan sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye, wanda yake dauke da wasu sanadarai da ke shake dan adam, wanda hakan ya sanya Falastinawa da dama suka galabaita, wasu kuma suka samu raunuka.

Yankunan Falastinawa da ke gabashin birnin Quds dai sun saba ganin irin wannan cin zarafi daga jami’an tsaron Isra’ila, wanda hakan kan sanya matasa su dauki matakin yin ruwan duwatsu da kona tayoyi, da hakan kan sanya yahudawan ala tilas su ja da baya.

3708214

 

 

 

 

 

 

captcha